Abinda ke nuna hakan shi ne yadda jigajigan jam'iyar ke barinta a wasu Jihohi kamar yadda ya faru jiya a Sakkwato dake arewa maso yammacin kasar.
Bayan ‘yan majalisar dattawa da suka fice daga jam'iyar APC mai mulkin Najeriya kwanannan a wasu Jihohi kamar kebbi, katsina, Bauchi da kuma barazanar ficewa da wasu Bayanai suka nuna wasu senatoci na kan hanyar yi, hakama jam'iyar na rasa wasu magoya Bayanta a wasu Jihohin kasar.
A jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin kasar jam’iyar ta rasa jigajigan ta da suka hada da ‘yan majalisar wakilai 2, Abdullahi Balarabe Salame da Yusuf Isa Kurdula, da kakakin majalisar dokokin jihar da dan majalisa daya, da tsofaffin ministoci 2 da wasu kusoshi a jam'iyar.
Alamu na nuna wadanda suka fice daga jam'iyar sun daura damarar fada da ita a zabubukan da ke tafe, kamar yadda tsohon Ministan Sufuri a Najeriya Yusuf Sulaiman ya fadi.
Ku Duba Wannan Ma Tsohon Minista Dalung Ya Bayanna Dalilin Da Ya Sa Ake Ficewa Daga APCSu kuwa jagororin jam'iyar PDP ficewar jigajigan APC ya kara musu karsashi, kamar yadda jagoran ta a Sakkwato, gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya nuna lokacin karbar wadanda suka shigo PDP.
Shi kuwa Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyar PDP kuma gwamnan jihar Delta Docta Ifeanyi Okowa da yake maraba da wadanda suka canja sheka zuwa PDP, bayan yayi tsokaci akan matsalolin da Najeriya ta samu kanta ciki a karkashin mulkin APC ya ce sun yunkuro ne domin su sake gina kasar a jam'iyar PDP.
“Ina son godewa ‘yan uwanmu da suka shigo cikin dangi na gari, jam'iyar PDP dangi ne wanda ya tsaya akan kyautata Najeriya, a zaman abu daya, mun godewa jagororin PDP na Sakkwato akan dawo wa da ‘yan uwanmu gida, wadanda suka hangi lokaci yayi da ya kamata a ceto kasarmu a kuma sake gina ta.....
Atiku yace yazo ne domin sake gina kasa da hada kan ‘yan kasa....”
Ku Duba Wannan Ma NASARAWA: Wasu ‘Yan Takara Sun Janye Daga Shiga Zabe Saboda Sauye-Sauyen Daliget Da Ake Zargin APC Ta YiMuryar Amurka ta tuntubi bangaren jam'iyar APC wadda ta rasa ‘ya'yanta ko ya ta ji da wannan lamarin?
Sambo Bello DanChadi shine kakakin ta a Sakkwato, ya kuma ce da ka zauna a gida kuma babu kwanciyar hankali, to gwamma ma baka gida. Bisa ga cewarsa, wasu ‘yan APC suna zaman sunan APC ne, amma ayyukansu ba na APC bane.
Sauya sheka tsakanin magoya bayan jam'iyun siyasa abu ne da ke faruwa a duk lokacin da iskar siyasa ta kada, sai dai wasu lokuta ba'a gane inda take sha sai anyi zabe an kare.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5