Kotun Daukaka Kara da ke birnin Sakkwato ta yanke hukunci cewa babu wata shaidar cewa jam’iyyar APC ta gudanar da zaben fidda ‘yan takara gabanin babban zaben Najeriya na 2019, wanda da wannan hukuncin, Kotun Daukaka Karar ta jingine hukuncin Babbar Kotun Gusau, wadda ta zartas cewa APC ta gudanar da zaben fidda ‘yan takara.
Hukucin na Kotun Daukaka Kara ya dadada ma jagoran ‘yan takarar gwamnan jahar Zamfara dinnan da ake wa lakabi da “G-8”, Sanata Kabir Garba Marafa, tare da sauran ‘yan takarar gwamnan karkashin jam’iyyar APC, wadanda su ka gabatar da karar, inda su ke kalubalantar hukuncin Babbar kotun jahar Zamfara, wadda ta tabbatar da cewa jam’iyyar ta APC ta gudanar da zaben fidda gwani.
Barrista Sirajo Garba Gusau wanda ke daga cikin lauyoyin da su ka halarci zaman kotun ta daukaka kara, ya kuma yi karin haske akan hukuncin da ta yanke da cewa na farko dai Babbar kotun na da hurumin sauraron karar da ‘yan takarar su ka gabatar saboda an tabbatar ‘yan takara ne karkashin jam’iyyar APC wadanda su ka cika ka’idoji ciki har da na sayen fom.
Lauya Sirajo ya kuma ce akwai takardar da Hukumar INEC ta tura ma Ciyaman din APC na Kasa Adam Oshiomhole cewa ba a yi zaben fidda gwani a Zamfara ba; kuma akwai takardar da shi kuma Oshiomhole ya tura ma hukumar zaben cewa APC za ta gudanar da zaben. Don haka, in ji Sirajo, kotun ta jingine hukumcin da ya gabata ba tare da bayyana dan takara na halal ko kuma makomar zaben APC da aka yi ba.
To sai dai wani masanin shari’a a jahar Sakkwato, lauya Kabiru Madawaki, ya ce dayake alamomin APC aka saka a lokacin zaben a maimakon ‘yan takara, jam’iyya kenan aka zaba ba wani mutum ba, don haka jam’iyyar na iya warware matsalarta daga baya.
To sai dai duk da yake kotun a karkashin jagorancin mai shara’a Tom Shu’aibu Yakubu, ba ta fito ta bayyana al’amari na gaba bayan hukuncin ba, to amma lauyoyin ‘yan takarar bangaren gwamnatin jihar sun ce za su daukaka kara zuwa kotu ta gaba.
Ga Murtala Faruk Sanyinna da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5