AKantocin kudi na jahohi da daraktoci da sauran manyan Jami’an tafiyar da harkokin kudi a ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya kana da takwararorinsu na jahohin kasar 36 da kuma birnin tarayya Abuja ne ke halartar taron na yini uku.
Babban akanta janar na tarayya Ahmed Idris, ya fayyace makasudun shirya taron, inda ya ce an shirya taron ne domin tattaunawa akan yadda za’a samar da sababbin hanyoyin da gwamnatocin jahohi da na tarayya za su bi domin samar da kudaden shiga.
Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ya ja hankalin mahalarta taron su kiyaye da ka’idojin da doka ta shimfida wajen tafiyar da dukiyar al’umar kasa.
Mataimakin gwamnan Kano Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, wanda ya wakilci gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ce aiwatarwa tare da sanya ido sosai akan tsarin nan na asusun kudi na bai daya ya bai wa gwamnatin jihar Kano damar like rariyar da kudade ke zirarewa a ma’aikatu da hukumomin gwamnati
Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu, ya nanata alakar da ke tsakanin ilimi da habaka tattalin arzikin kowace al’uma, Ya kuma yi kira ga gwamnatoci da su bai wa fannin ilimi kulawar da ta dace.
Ga Rahoto Mahmud Ibrahim Kwari Cikin Sauti
Your browser doesn’t support HTML5