Mallam Isah Garba shine jamiin cibiyar da ta shirya wannan taron kuma yayi bayanin makasudin wannan taron.
‘’Dalili shine cewa mun faro tun daga lokaci da aka fara hidima na siyasa to daga fara hidimar ne sai muka cewa siyasar ta koma wani iri ana neman a keta Najeriya bangare-bangare, wannan bangare na sukan wannan bangare da kalamai marasa dadi da kuma mutane masu tasiri cikin al’umma sukan yi maganganu kuma da zasu iya tunzura al’umma din, sai muka ga hanya data fi dacewa shine mu san yadda zamu yi, mu a tana mu bangaren mu dode wannan, to kaga a wnan muna neman yan jarida ne musammam masu aiki gidan radio wadanda sune suke bada dama ta hanyar su ne masu wadannan maganganu suke isa al’umma, idan da basu bada dama to al’umma ba zata ji abinda aka fada ba, to kuma komi munin abinda aka fada idan dai ba aji shi ba, to bai zama mummuna ba.’’
To sai dai da aka tambaye shi baijin wannan yayi karo da fadan albarkacin baki ba?
‘’Shine sai yace yancin fadin albarkacin baki daban, haka kuma tunzura al’umma daban duk lokacin da ake batun al’barkacin baki, a lokaci guda kuma ana kiyaye abinda zai tunzura wani lokacin da kake da yanci, yancin naka bai baka damar ka tunzura wani ba.’’
Shima Mallam Abdulganiyu Rufai Aliyu Gaya Programe Officer yayi Karin haske game da yadda za a tantance kalamai da kla iya sa yin tunzuri.
Ga Abduwahab Mohammed da ci gaban labarin ‘’4 02’’
Your browser doesn’t support HTML5