Wadanda aka kame din na cikin jerin ma’aikatan da ke raba kayan abinci ga manoman da talauci yayi wa katutu a arewacin yankin Jowzjan a ranar 8 ga watan Fabrairu, a yayin da aka yi musu kwanton baunan da ake zargin yan kungiyar Da’esh ne suka kai harin.
Kamar yadda jami’an tsaron Afghanistan suka ce, maharan sun kashe ma’aikatan kungiyar Red Cross din guda shida kafin su tafi da biyu daga cikin zuwa wurin da ba’a sani ba.
Kungiyar agajin ta dakatar da duk wasu harkokinta na taimakon jin kai a fadin kasar da miliyoyin mutane ke bukatar tallafin gaggawa sakamakon hare-haren 'ya'yan kungiyar Taliban da suka yawaita.
Monica Zanarelli shugabar ICRC ta fada a wani rubutaccen sako da ta bayar a yau asabar cewa, “Muna kira ga wadanda suka kama mana abokanan aikinmu da su tausaya su sako mana su lafiya ba tare da wani sharadi ba, kuma kada su saka rayuwarsu a cikin hadari. Ta kara da cewa “Bama son bakin cikin ya kara yi mana yawa.”
Zanarelli tayi kira ga hukumomi da jami’an tsaro da ke aiki a arewacin Afghanistan da su taimaka wajen ganin an sako ma’aikatan na kungiyar Red Cross lafiya. Wannan shine hari mafi muni da ya taba faruwa akan ma’aikatan kungiyar a cikin kasar.