Gwamnatin kasar Hunduras ta jingine wasu dokokin ta , kana ta samar da dokar hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa shidda na safe domin baiwa jamiaain tsaro damar gudanar da dukkan ayyuka su da suke bukatar aiwatar wa sabo da shawo kan masu zanga-zanga da ya barke sakamakon zaben shugaban kasa da akayi ranar lahadin data gabata wanda ya haifar da rudani a cikin kasar.
Daya daga cikin ministocin kasar Ebal Diaz yace an dage dokar kasar ce, domin ya baiwa sojoji da ‘yan sanda su samu damar shawo kan rikicin da ya kunno kai a kasar sakamakon zaben.
Shugaban kasar na yanzu Juan Orlando Narnendez, yace hakan zai baiwa jamiaan tsaron damar samar da zaman lafiya cikin kasar.
Harnandez dai shine shugaban kasa na farko da zai tsaya takara zagaye na biyu tun bayan da babban kotun kaar ta dage dokar hana sake tsayawa takara.
An dai fara zanga-zanga ne tun a ranar jumaa lokacin da hukumar zabe ta fara kidayar kuria, da ake tuhumar akwai toge a cikn sa na zaben da aka yi ranar lahadi.
Magoya bayan Salvador Nasralla mai raayin rikau na jamiyyar adawa dake da goyon bayan jamiyyar maiu yaki da mulkin kama karyane a ranar jumaa suka datse hanya suka banka wa tayoyi wuta suka shiga ko fita cikin babban birnin kasar na Tegucigalpa.
Kanfanin dillacin labarai na Reuters yace jamiian tsaro ne suka kai doki ga fadar shugaban kasar, wanda keda goyon bayan gwamnatin Amurka.
Mahulkun tasunce daya daga cikin masu zanga-zangar ya mutu, yanzu dai zanga-zangar yau yana cikin kwana na 6 kenan.