Annobar COVID-19 Ta Shafi Harkokin Siyasa a Afurka

Masu nazarin annobar coronavirus sun ce annobar ta shafi yanayin siyasa da kuma zabuka a kasar Afurka kamar yadda abin ya ke a sauran wurare, ta kuma janyo jinkirtawa da kuma dage zabuka a wasu wuraren.
Masu nazari kan harkokin siyasa din sun kuma ce, annobar ta kuma bai wa shugabanni damar amfani da farbagar da jama'a su ka shiga wajen yinkurin dada zama bisa karagar mulki.
A kalla kasashen afirka 9, ciki harda Najeriya, Kenya, da Zimbabwe sun dage wasu zabukansu sakamakon tsoron yaduwar cutar inji kungiyar da ke kula da yanayin zabuka a duniya.
Kasar Habasha na cikin wannan jerin yayin da ta dage zabukan ta wadanda ya kamata a yi a ranar 29 ga watan Agusta, duk da cewar jam’iya mai Mulki ta Tigray ta ce dole sai ta gudanar da zaben.