Annobar COVID-19 Na Kara Bazuwa a Kasashen Turai Da Yawa

C0VID-19

Mako guda bayan da mace-mace sakamakon coronavirus suka zarta miliyan 1, an samu sama da mutane miliyan 35 da suka kamu da COVID-19 a kasashen duniya, a cewar Cibiyar samar da bayanan Coronavirus ta Johns Hopkins. 

Kasashen Turai da yawa suma sun kai matakin annobar na tarihi inda A yau Litinin Jamus ta bada rahoton cewa an samu mutane fiye da 300,000 da aka tabbatar sun harbu da cutar ita kuma Birtaniya ta ba da rahoton akalla mutum 500,000.

Kamfanin cinimar Cineworld na Birtaniya, wanda shine kamfanin cinima mafi girma na biyu a duniya, a yau Litinin ya sanar da cewa zai rufe gidajen cinimansa da ke Birtaniya da Amurka.

Dokar kulle sanadiyar Coronavirus da kuma takaita taron jama’a da aka sanya sun shafi masana'antar sosai. Kamfanin Cineworld ya ce matakin zai shafi ayyuka 45,000.

Don shawo kan rasa ayyuka a kasar, a yau Litinin gwamnatin Birtaniya ta kaddamar da wani sabon shiri na dala miliyan 300 da nufin taimakawa mutane su koma aiki.