Anji Harbe-Harbe da Tashin Boma-Bomai

Sojojin ruwan Najeriya suke karbar horo dagsa sojojin ruwan Amurka.

Rahotani na nuni da cewa hankali ya fara kwanciya a garin Chibok ganin yanda yawan jami'an tsaro ya karu a garin
Yanzu hankali ya fara kwanciya a garin Chibok,ganin yanda yawan jami’an tsaro ya karu a gari.Inda dakarun kasashen waje suka fara sauka a garin na Chibok.

Rahotanin da muryar Amurka ta samu na nuni da cewa Kamar karfe tara na safe anji harbe-harbe da tashin boma-bomai a cikin dajin,kusa da dajin sambisa,wanda ake zaton sojoji ne ke dauki badadi da 'yan boko haram.

Ko da yake wadanda ake nema wato’yan boko haram sun bazu inji malam Shettima a wani hira da suka yi da wakilin muryar Amurka Aliyu Mustapha ta wayan harho.

Ya kara da cewa dakarun kasashen waje da hadin gwiwa sojojin Najeriya tuni sun fara tunkaran kalubalen dake gabansu na yakar ‘yan boko haram.

Yace bukatar su shine yanda za’a kwato wadannan yara daga hannun wa wadannan bata gari,ko dai yake iyaye yaran,har yanzu na tattare da bacin rai.

Your browser doesn’t support HTML5

Anji Harbe-Harbe Da Tashin Boma-Bomai - 4'50"