Ander Herrera: Zan Sauya Sheka Don Cinmma Burina A Wasa

Dan wasan tsakiya na Manchester United Ander Herrera, mai shekaru 29 da haihuwa, ya cimma kwarya-kwaryar matsaya tsakanin sa da kulob din Paris-saint German, domin komawarsa kungiyar don ci gaba da taka leda tare da ita.

Hakan ya biyo bayan Manchester United ta ki amincewa da bukatansa, na karin albashi da yake so Manchester tayi masa in har tana bukatar da ya zauna a kungiyar.

Mujallar da ta ruwaito ta ce, dan wasan ya dauki wannan matakin ne bayan rashin gamsuwa da albashin da Manchester United za ta ci gaba da ba shi a karkashin sabuwar yarjejniyarsa da ita. Manchester United na biyan dan wasan kudi fam dubu 80 a kowace mako.

Shi kuwa dan wasan Herrera, yana bukatar a kalla ta rika biyan sa fam dubu 200 a duk mako kafin ya zauna.

Inda ita kuma Manchester United tayi watsi da wannan bukatun dan wasan duk da cewa, yana cikin zaratan 'yan wasan da sabon kocinsu, Ole Gunnar Solskjaer ke ji da su.

Kocin na Manchester Solskjaer, ya bayyana Herrera a matsayin dan wasa mai kuzari da juriya, wannan dalilin ya sanya kocin yanke burin ci gaba da aiki da shi.

Dan wasan ya zo kungiyar Manchester United ne a shekarar 2014, daga Atletico Madrid, ya samu nasarar zurara kwallaye 12 a cikin wasanni 130, da ya buga a kungiyar