Anci Zarafin Dan Wasa Divock Origi Lokacin Karawarsu Da Genk

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool tayi Allah wadai da abunda magoya bayan kungiyar kwallon ta Genk su kayi wa dan wasanta Divock Origi, na sanya kyalle da ke nuna wariyar launin fata.

A ranar Laraba da ta gabata ne Liverpool tayi tattaki zuwa kasar Belgium, domin karawa da kulob din Genk, cikin gasar zakarun turai UEFA champion league, a matakin wasan rukuni zagaye na uku, inda Liverpool ta samu nasara da ci 4-1.

Anyi hanzari don cire kyallen kuma yanzu haka ana aiki tare hukumomi dan tantance wadanda ke da alhakin aikata wannan lamari, da ya addabi 'yan wasa bakaken fata dake nahiyar turai.

Dan wasan Origi mai shekaru 24 da haihuwa, ya shafe shekaru tara tare da kungiyar kwallon kafa na Genk, bangaren matasa daga bisani ya koma Lille a shekara ta 2010, inda yanzu yake taka ledarsa a kungiyar Liverpool ta kasar Ingila.

Origi ya kasance a benci lokacin da aka fara wasan na ranar laraba. Itama a nata bangaren hukumar 'yan sanda ta Belgium tace zata hada hanu da Liverpool, domin nemu wadanda suke da hanu kan lamarin domin daukar mataki a kai.