Yau Asabar Dubban ‘yankasar Zimbabwe ne suka hau titunan birnin kasar na Harare suna zanga-zanga inda suke kira ga shugaba Mugabe da yayi murabus.
Masu zanga-zangar suna dauke da kwalaye da rubuce-rubuce iri daban-daban .
Sojojin kasar wadanda da farko suke hana zanga-zangar a fadar gwamnatin kasar, yanzu suna mara wa masu zanga-zangar baya, wanda su da kansu ne ke baiwa masu zanga-zangar umurnin su isa babban Filin taron kasar inda za a gudanar da jawabai daga shugabannin kare hakkin bil adama, ‘yan siyasa, ciki ma harda tsohon madugun ‘yan adawa da yake kiran shugaba Mugabe da yayi murabus.
Wannan filin taron dai shine sanannen filin dake cikin kasar inda nan, ne dubban ‘yan kasar suka yi wa shi Robert Mugabe barka da zuwa bayan ya dawo daga gudun hijira a shekarar 1980 bayan kamala yakin neman yancin kasar daga tsirarun fararen fata.
Haka kuma zanga-zangar bai tsaya a cikin babban birnin kasar ba domin harda wasu birane na kasar suna gudanar da irin wannan zanga-zangar na kawo karshen mulkin shugaba Mugabe.
Yanzu haka ana ci gaba da kiki-kaka da shugaba Mugabe,da sojoji,’yan siyasa harma da ‘yan jamiyyar sa ta ZANU –PF,’Yan rajin kare demokaradiyya, na ya sauka amma ya kekasa kasa yace a’a
Mugabe dan shekaru 93 da haihuwa ya kwashe shekaru 37 yana mulkin kasar.
Jami’an maaikatar tsaron kasar ne dai suka karbe mulkin kasar kana suka karbe ikon wasu muhimman maaikatu da hukumomi kana suka yiwa shugaba Mugabe daurin talala, sai kuma suka kame wadanda suke dauka a matsayin barayin gwamnati dake kewaye da shugaban ciki ko harda Farfesa Jonathan Moyo, da Ministan harkokin cikin gida Ignatius Chombo,sai kuma ministan kananan hukumomi Saviour Kasukuwere, da Sakataren kungiuyar matasa jamiyyar su ta ZANU PF Kudzanayi Chipanga da dai wasu da dama.