Jami’an Mali na binciken barkewar cutar da ake zaton zazzabin Ebola ne, bayan barkewar cutar a wannan yanki.
WASHINGTON, DC —
Ministan harkokin kiwon lafiya na Mali yau Juma’a ne ya bada tabbacin wannan bincike.
Yanzu dai jami’an kiwon lafiya daga can Mali sun aiko da samfurin jini nan Amurka birnin Altlanta a gwada. A halin da ake ciki yanzu, an kebe mutanen su uku, inda za’a yi musu magani.
Jiya Alhamis Hukumar Lafiya ta Duniya tace jami’ai a yammacin Afirka sun bada rahoton tabbacin barkewar wannan cuta inda mutane sama da 130 yanzu ake zaton suna dauke da cutar, mafi yawancinsu a kasar Guinea.
Hukumar ta kara da cewa cutar dai yanzu ta jawo asarar rayuka 83 a kasar Guinea, da kuma 5 kasar Liberia.