Bangorin da aka yi amannar wani ballin fikafikinsa ne, an nufi kasar Faransa don yin bincike akai don gano gaskiyar kokwanton da ake. Kamfanin da yak era jirgin sun ce zasu shiga Faransa bisa neman izinin hukumomi don taya bin diddikin wannan lamari na jirgin da ya salwantar da mutanen cikinsa 239.
Mabincikan kasar Australia ma sun ce suna kyautata zaton bangorin jirgin ne na Malaysian Airline. Kamar yadda babban kwamishinan hukumar kula da lafiyar safarar kasar Australiyan Martin Dolan ya fadawa manema labarai a jiyan.
An dai tsinto ballin ne mai mita biyu a ranar Larabar data gabata daga bakin tekun tsibirin Reunion Island dake gabashin kasar Madagasca. Haka kuma kimanin tazarar kilomita 3,500 daga inda aka ji duriyar jirgin ta karshe a na’urar sadarwar da ke bin diddikin tafiyar jirage.