Ana Zargin Yari Da Ture Wani Ma'aikacin FAAN

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul'aziz Yari

Ana zargin tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari da ture wani ma'aikacin muhalli wanda ya yi kokarin aikinsa domin takaita yaduwar COVID-19.

A cikin wata sanarwar da hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta FAAN ta fitar ta ce Yari ya ci zarafin ma'aikacin wanda ya yi kokarin goge akwatin tsohon gwamnan lokacin da zai yi tafiya a filin jiragen sama na Malam Aminu Kano a ranar Asabar.

A cewar FAAN, Yari ya ture ma'aikacin ne sabili da a cewar shi, s"shi babba ne, saboda haka bai kamata a wannan aikin ya shafe shi ba."

FAAN ta yi alla wadai da halin Yari kuma ta ce ba za ta lamunci hakan ba.

Yayin da aka dawo da zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya bayan dakatar da aiki tun watan Maris domin takaita yaduwar cutar coronavirus, ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya umarci dukannin manya da kuma gwamnoni da su bi sabbin dokokin da aka gındaya a dukkanin tashoshin jiragen.