Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International da kungiyar kare hakkin dan adam ta Angola OMUNGA, na zargin jami’an tsaro da kashe akalla mutane bakwai.
WASHINGTON D.C. —
Sun zarge su ne da yin hakan yayin aiwatar da dokar hana zirga-zirga, sanadiyyar COVID-19 a kasar da ke kudancin Afurka.
Jiya Talata, kungiyoyin kare hakkin biyun su ka yi kiran da a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Matasa da kananan yara bakwai ne dai suka mutu, tsakanin Mayu da Yuli. Karamin cikinsu na da shekaru 14.
A sanarwar da kungiyoyin suka fitar sun ce, "jami'an tsaro a Angola sun yi amfani da karfin wuce gona da iri yayin da suke fuskantar keta dokar ta-baci da aka sanya, don shawo kan yaduwar COVID-19," a cewar sanarwar.