Ana zargin Prime Ministan Isira'ia da laifin cin hanci da kuma zamba

Prime Ministan Isira'ila Benjamin Netanyahu

Ana zargin Prime Ministan Isira'ila da laifin hannu a wasu laifuffukan da suka danganci cin hanci da zamba

Ana zargin Prime Ministani Ministan Isra’ila Benjmin Netanyahu da laifin cewa yana da hannu, cikin wasu laifuffukan da suka danganci cin hanci da zamba da cin amana a cikin wasu batutuwar rashawa guda biyu.

Masu binciken da suka yi watani suna yiwa Netanyahu tambayoyi, a jiya Alhamis sun nemi izinin kotu akan hana yan jarida daukan rahotanin a kan wadannan batutuwan rashawa

Netanyahu ya musunta aikata laifi kuma mai Magana da yawunsa ya fada a wata sanarwa a jiya Alhamis cewar wannan wani yunkurin bita da kulli ne ake yiwa Pirayi Ministan, da nufin kokarin canja gwamanti.

Netanyahu dai ba shine shugaban Isra’ila na farko da ya fara huskantar binciken aikata laifi ba, tsohon Pirayi Minista Ehud Olmert, an yanke masa hukunci cin amana da cin hanci a shekarar 2014, shima Ariel Sharon ya sha tambayoyi yayin da yake a ofishi a kan zarge zargen cin hanci da samun kudaden yakin neman zabe na haram.