Ana zargin kungiyar ISIL da laifin amfani da makamai masu guba

Mayakan kungiyar ISIL

Kungiyar kasa da kasa dake hankoron haramta amfani da makamai masu guba da ake cewa OPCW , wadda take da alhakin binciken keta haramcin tace a shirye take ta bi diddigin ikirari ko kuma zargin da aka yi cewa mayakan kungiyar ISIS suna amfani da gas masu guba akan sojojin Kurdawa a Iraq.

Wata kungiyar kasa da kasa dake hankoron haramta amfani da makamai masu guba da ake cewa OPCW a takaice, wadda take da alhakin binciken keta haramcin tace a shirye take ta bi diddigin ikirari ko kuma zargin da aka yi cewa mayakan kungiyar ISIS suna amfani da gas masu guba akan sojojin Kurdawa a Iraq.


Mai magana da yawun kungiyar, yace a shirye kungiyar take ta dauki mataki da zarar kasar Iraq, wadda take cikin kungiyar ta nemi taimakon yin hakan.


A baya an zargin kungiyar ISIS da laifin amfani da makamai masu guba, to amma al'amari na baya bayanan anyi zargin cewa a wannan makon ya auku. Jamian tsaon kasar Jamus sunce kimamin mayakan Kurdawa sittin ne suka kusanci gas din da aka haramta amfani dashi a lokacinda suka fafata da yan yakin sa kan kungiyar ISIS a ranar Laraba.


Mai magana da yawun kungiyar yace ya zuwa yanzu kungiyar sa bata samu rahoto akan amfani da wannan gas daga wata kasar dake cikin kungiyar ba. To amma yace ya kamata shugabanin Iraqi su bi diddigin wannan al'amari bisa rahotanin da ake samu daga kafofin yada labaru.


Dukkansu da kasar Jamus wadda take baiwa sojoji Kurdawa horo da kuma Amirka, babu kasar data gabatar da shedar amfani da gas mai guba a Iraq ga wannan kungiyar da ake cewa OPCW a takaice.