Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya na nuna cewa Korea ta arewa ta kai wasu kayayyaki a Syria da ta yi wu gwamnatin Bashar al-Assad ta yi amfani da su wajen yin makamai masu guba.
Rahoton ya ce wasu abubuwa kamar na'urar auna yanayi da sauransu na cikin akalla kayayyaki 40 da ba a ba da rahotonsu ba da Korea ta arewa ta kai Syria a tsakanin 2012 da 2017.
An ba wasu kafafen yada labarai wannan rahoton a daidai lokacin da Amurka da wasu kasashe ke zargin gwamnatin ta Syria da yin amfani da makaman guba akan farar hula.
An ga kwararru a fannin kimiyar makamai masu linzami na Korea ta Arewa na aiki a wuraren kera makamai masu guba da masu linzami na Syria, a cewar rahoton, wanda wasu kwararru da suka yi binciken kwakwaf akan yadda Korea ke kiyaye takunkumin Majalisar Dinkin Duniya.