Bayanai sun yi nuni da cewa an kama shi ne saboda tsokaci da ya yi a kafar Twitter inda ya nuna gazawar gwamnatin Muhammadu Buhari bayan sace ‘yan matan Jangebe ya kuma yi kira ga shugaban da ya sauka daga mulki.
"Ya nuna karara cewa, mu a matsayinmu na gwamnatin APC a kowane mataki, mun gaza a aiki na farko da aka zabe mu yi, wanda shi ne samar da tsaro ga rayukan jama'a da kare dukiyoyinsu. Ba bu rana guda da za ta wuce da ba za a ji wata matsalar tsaro ta taso ba a wannan kasa. Wannan abin kunya ne! a dauki mataki kan 'yan ta'adda ko ka yi murabus" Sakon na Yakasai na Twitter ya ce, wanda tuni ya goge shi.
Wadannan kalaman nasa, sun sa gwamnatin jihar ta Kano ta sallame shi kamar yadda kwamishinan yada labaran jihar Muhammed Garba ya fitar a wata sanarwa.
A ranar Juma’a wasu ‘yan bindiga suka sace dalibai 317 a makarantar kwana ta mata zalla da ke Jangebe a hukumar Talatar Mafara a jihar Zamfara, lamarin da ya janyo kakkausar suka a ciki da wajen Najeriya.
Yakasai, da ne ga fitaccen dan siyasa kuma daya daga cikin dattawan arewa Alhaji Tanko Yakasai.
Wannan ba shi ne karon farko da Yakasai wanda aka fi sani da @dawisu a Twitter yake sukar gwamnatinsu ta APC ba, wacce ita ke mulki a Kano karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
A watan Oktoban shekarar da ta gabata ya taba sukar Buhari kan zanga zangar Endsars da ta mamaye wasu sassan kasar lamarin da ya sa har aka dakatar da shi daga aiki.
Kafafen yada labaran na Najeriya da dama sun ruwaito cewa a ranar Juma’a Yakasai ya yi ta wallafa sakonni daban-daban yana mai nuna gazawar gwamnatin ta Buhari wajen shawo kan matsalar tsaro da ta addabi kasar.
Sai dai hukumar ta DSS reshen jihar Kano ta musanta cewa ita ta kama Yakasai.