Dokar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fitar na haramatawa wasu yan kasar su 50 fita zuwa kasashen wajen na cigaba da jawo cece-kuce a kasar.
WASHINGTON, DC —
Su dai wadannan mutane ana tuhumar su da yin ruf da ciki da kwanciyar magirbi da dukiyar kasa, abinda yasa aka umarci jami’an tsaro da su sa ido akansu don kada su samu damar sulalewa zuwa kasar waje.
Tun fako, wadansu jaridun kasar har sun buga sunayen wasu mutum 50 da dokar zata shafa, ciki har da matattu, to amma kuma sai daga baya fadar shugaban kasar ta musanta batun cewa an zayyano sunayen wadanda lamarin ya shafa.
Tuni ‘yan adawa suka bayyana daukar wannan matakin a matsayin siyasa, suka kuma bayyana daukar matakin a matsayin wani salon yakin neman zabe.
To sai dai kuma ,yayin da wasu ke zargin gwamnatin APC da bita da kulli da kuma wata manufa a yaki da cin hancin da rashawan, su kuwa kusoshin jam’iyar ta APC, na ganin ba haka lamarin yake ba.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul’aziz
Martani Kan Hana Wadansu fita Daga Najeriya-3:25"