Da farko ya fara yiwa Sahabun bayani ne game da fitowar Jamaa, ga kuma abinda yake cewa.
‘’Wato akwai inda aka bude karfe 7 akwai inda aka bude 7:15 akwai kuma 7:30 an bude su akan lokaci kuma ba’a samu wani matsala ba, har zuwa wannan lokacin.’’
Da kuma Sahabun ya tambaye shi ko yaya fitan jamaa ida an kwatanta da zaben farko anan ko sai Alhaji Amadu ya amsa da cewa.
‘’Lallai dai akwai matsala game da wannan kuma ince babba saboda mutane basu fito ni ina cikin babban birnin kasar wato Cotonou, mu mun fita kuma munyi zabe kuma munyi zabe, munga cewa mutane basa fitowa.’’Sai kuma Sahabun ya sake tambayar sa ko me yasa yake ganin mutane basu fito ba?
‘’Yace dalilin dai an samu ba zata ne domin ko wadan da akayi zaton zasu zo zagaye na biyu bashi ne yazo ba.
Ga ci gaba da tattaunawar tasu 3’16
Your browser doesn’t support HTML5