Ana Zaben Shugaban Kasa a Togo

Shugaban Togo, Faure Gnassingbe yayin taron ECOWAS a 2015. REUTERS.

A yau Asabar al'umar kasar Togo ke kada kuri'a a zaben shugaban kasa , zaben da masu lura da al’amuran siyasa ke hasashen Shugaba Faure Gnassingbe ne zai lashe.

Sama da shekara 50 iyalan shugaban suka kwashe suna mulkin kasar ta Togo.

A shekarar 2005, shugaban na yanzu ya gaji mahaifinsa Eyadema, wanda ya kwashe shekara 40 akan mukamin.

Gnassingbe ya taka muhimmiyar rawa a sauya fasalin kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya amince da tsarin yin wa’adi biyu na shekara biyar-biyar.

Sai dai wannan sauyi bai yi tasiri ba; abin da ake ganin zai ba shugaba Gnassingbe damar zama akan karagar mulki har nan da shekarar 2030.

'Yan takara shida ne ke hamayya da shugaba mai ci, ciki har da Jean-Pierre Fabre wanda ya zo na biyu a yawan kuri'u a zabukan 2010 da kuma 2015.