Masu kada kuri’a a Mauritania sun dunguma zuwa rumfunan zabe a yau Asabar, a zabe na farko da za a yi, wanda babu shugaban kasar mai ci a matsayin dan takara.
Rabon da a ga haka, tun bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar 2008.
Da misalin karfe takwas na safe aka bude rumfunan zabe a sassan kasar wacce ke yankin Hamada, kuma za a kai har bakwai na dare kafin a rufe su.
Shugaba Mohammed Ould Abdel Aziz zai sauka daga mukaminsa, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, bayan kammala wa’adinsa na biyu na shekaru biyar-biyar.
Jam’iyyarsa ta UPR ta tsayar da tsohon ministan tsaron kasar Mohammed Ould Ghazouni a matsayin dan takararta.
Sai dai bangaren ‘yan adawa na zargin cewa ba za a ga wani sauyi daga gwamantin da za ta shude ba, sauyin da suka ce kasar na matukar bukatar.
Daga cikin ‘yan takarar da ke kalubalantar Ghazouni, akwai Sidi Mohammed Ould Boubacar, wanda tsohon firai ministan kasar ne, kuma jagoran adawa, wanda ke samun goyon bayan jam’iyyar Tewassoul.