Shugaban kasar Malawi Peter Mutharika na neman wa’adi na biyu yayin da masu kada kuri’a suka dunguma zuwa rumfunan zabe a yau Talata.
Kusan mutum miliyan 6.8 ake sa ran za su yi zabi tsakanin shugaba mai ci Mutharika mai shekaru 78 da ko mataimakin shugaban kasa Saulos Chilima.
Har ila yau akwai Lazarus Chakwera wanda a da mai wa’azi ya koma harkar siyasa.
Wadannan ‘yan takarar da ke kalubalantar shugaba Mutharika, sun yi alkawarin magance matsalar cin hanci da ta addabi kasar ta Malawi da ke kudancin Afrika.
Shi kuwa Mutharika, ya gina yakin neman zabensa ne bisa alkawarin bunkasa tattalin arzikin kasar da fannin ababan more rayuwa.
A shekarar da ta gabata, mataimakin shugaban kasa Chilima ya fice daga jam’iyya mai mulki ta Democratic Progressive Party, ya kafa wata jam’iyya da ta fi mayar da hankali kan matasa.
Matasa a Malawi su ne suka fi yawa a adadin masu kada kuri’a a kasar.