Ana Zaben Shugaban Kasa A Afghanistan

Afghanistan Elections

An fara kada kuri’a a zaben shugaban kasa a Afghanistan, yayin da ake fargabar gargadin da mayakan Taliban suka yi na cewa za su kai hare-hare a rumfunan zabe.

Mayakan sun yi kira ga masu kada kuri'ar kasar da yanwansu ya kai miliyan 9 da su zauna a gidajensu ko kuma su fuskanci fushinsu.

Hukumomin kasar sun ce, wata fashewa da ta auku a yau Asabar a wata rumfar zabe a birnin Kandahar da ke kudancin kasar, ta jikkata mutane da dama.

An dai jibge dubban jami'an tsaro a sassan kasar domin kare lafiyar masu kada kuri'a a rumfuna zabe sama da 4,000.

An samu wasu 'yan kasar ta Afghanisatn da suka ki fita zabe saboda fargabar hare-hare da wadanda suka yi ikrarin za a yi magudi a zaben.