A karon farko tun bayan korar mayakan ISIS daga kasar Iraki 'yan kasar sun kada kuri'ar zaben Majalisar Dokokin kasar
WASHINGTON D.C. —
Masu kada kuri’a a kasar Iraq sun garzaya rufunan zabe a yau dinnan Asabar don kada kuri’a a zaben kasa na farko tun bayan da aka fatattaki kungiyar ISIS daga kasar bara.
Masu kada kuri’a na zaben ne daga cikin ‘yan takara 7,000 da ke takarar kujeru 329 na Malisar Dokokin kasar.
Dama an kafa rufunan zaben a fadin kasar, ciki har da sansanonin ‘yan gudun hijira masu dauke da mutane kimanin miliyan 3 wadan da yakin ISIS da sauran yake-yake su ka raba su da muhallansu.
Ko bayan an sanar da sakamakon zaben na yau Asabar, za a shafe watanni ana tattaunwar kafa gwamnati kafin sabuwar gwamnatin ta kahu.