Mai gabatar da kara na musamman dake kotun duniya na Hague ya tuhumi shugaban kasar Kosovo Hashim Thaci da wasu mutum 9, da laifuka 9 da suka danganci cin zarafi da laifukan yaki da suka aikata lokacin yakin neman 'yancin kasar.
Rahotanni daga ofishin mai tuhuma na nuna cewa, wadanda ake tuhuman sunyi sanadin kisan kusan mutane 100 tare da tilasta bacewar wasu da azabtarwa da kuma zaluntar daruruwan jama’a wadanda suka hada da ‘yan Albenia, Serbia da Roma dake Kosovo.
Ofishin ya kara da cewa tuhumar sakamakon bincike ne da aka gudanar na tsawon lokaci kuma ya nuna jajircewar mai gabatar da karar ne na ganin ya tabbatar da tuhuma da ake musu.
Wani alkali na musamman zai duba tuhumar domin tabbatar da hukuncin kafin babbar shariar da zai zartar.
Wani jami’in tsaron Amurka ya bayyana wannan tuhuma da aka sanar a jiya Laraba wanda ya dau shekaru 20 ana hadawa, a matsayin babban cigaba a kokarin tabbatar da adalci da sulhu a yankin na yammacin Balkan. Ya kara da cewa, an dauki wannan matakin ne domin ganin an yi wa ‘yan Kosovo wadanda aka zalunta adalci da kuma ciyar da kasar gaba.