Sabon tsarin hayar mota tasi na zamani na masu kudi da aka bullo da shi a garin Kaduna na gamuwa da suka da yawaba daga bangarori daban-daban. Alhaji Musa Zubairu ya gaya ma abokin aikinmu Usman Kabara cewa tsarin na cike da katsalandar din gwamnati. Ya kuma ce ba a yi ma mutane cikakken bayanin tsarin da kuma dalilan shiga gwamnati ciukin tsarin ba. Amma da aka ja hankalinsa kan farashin hayar motar na dubu biyu kan sa’a guda, ya amince cewa tsarin zai fi amfanar masu kudi ne akasari, ya kara da cewa tun da ba a soke tsarin da aka saba da shi ba, talaka zai iya cigaba da amfani da tsohon tsarin.
Amma Alhaji Zubairu ya ce sabon tsarin na da amfani sosai muddun dai bata gari bas u shigo ciki ba. Y ace idan bako ya zo Kaduna ya na da tabbas cewa kayansa ba za su salwanat ba. Amma ya kamata a yi bayani cewa ba don talaka aka yi ba saboda a daina cece kuce.
To amma kuma ya ce a dau matakan tabbatar da tsaron lafiyar wadanda ake daukawa a wannan sabon tsarin saboda kar miyagu su cutar da baki ko duk wani mai amfani da wannan sabon tsarin.
Ga cikakkiyar tattaunawar:
Your browser doesn’t support HTML5