Ana Shirin Maido Da Tattaunawar Sulhu Da 'Yan Taliban

Rahotanni sun bayyana cewa wasu wakilan kungiyar Taliban sun gana da Zalmay Khalizad, wakilin Amurka a shirin kawo sulhu a Afghanistan a farkon watan nan. Ganawar da aka ce an yi, a lokacin wata ziyara da ‘yan Taliban suka kai Islamabad don ganawa da jami’an Pakistan aka yi ta.

Wannan ita ce ganawar farko tsakanin Amurka da ‘yan Taliban da aka sani tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya soke tattaunawar samar da zaman lafiya da mayakan a watan Satunban da ya gabata, a cewarsa saboda ci gaba da tada zaune tsayen da mayakan suke yi a Afghanistan a kokarin su na kara samun tudun dafawa a zaman tattaunawar sulhun da ake yi.

Wani babban jami’in kasar Pakistan, wanda ya so a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin bayani akan batun, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa Pakistan ta taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan ‘yan Taliban ta hanyar nuna masu muhimmancin da ganawar ke da shi a shirin samar da zaman lafiyar.

A halin da ake ciki kuma, Sakataren harkokin wajen Amurka Mark Esper ya isa kasar Afghanistan, ziyarar da ba a sanar ba, a daidai lokacin da ake kokarin sake maido da tattaunawar samar da zaman lafiya da ‘yan Taliban.

“Makasudin ganawar shine a samu a cimma yarjejeniyar zaman lafiya, yarjejeniyar siyasa, wannan ita ce hanyar da ta fi dacewa,” abinda Esper ya fadawa manema labaran dake tafiya da shi kenan a yau Lahadi.