Ana Shirin Kammala Bukukuwan Ista A Ghana Yau Litinin

Ista a Accra

Yau Litinin ake shirin kammala bukukuwan Ista da Kiristocin duniya ke yi na tuna da daya daga cikin tushen imanin Kirista: mutuwar Yesu da kuma tashinsa daga matattu, bikin da aka dauka babban al’amari a Ghana, inda Kiristoci ke shirya yadda za su gudanar da wadannan ranakun Ista masu muhimmanci.

A Ghana, majami'u daban-daban sun gudanar da bikin Palm Sunday da jerin gwanon mambobinsu kan wasu manyan tituna, ranar da ake fara bukin, suna kada rassan iccen kwakwa da fararen kyalle suna rera waka. Sai ranar Juma’a, wato Easter Friday, suka je coci domin gudanar da ibada.

Easter in Accra Church Service

Fasto Felix Nze na cocin Portal of Fire and Deliverance Ministry dake Accra ya ce, ana tunawa ne da kisan da aka yi wa Yesu a ranar Juma’a da kuma murnar tashinsa daga matattu ranar Lahadi domin ya ceci al’umma, a ranar Litinin ne kuma da ake ziyartar ‘yan uwa da abokan zumunci da kuma mikawa juna kyaututtuka.

Wasu suna sa tufafin makoki masu duhu don tunawa da mutuwar Yesu Kristo. Haka kuma wasu sassa na Ghana suke nuna farin ciki da nasara don Yesu ya mutu domin zunubansu, kuma ya yi nasara a kan mutuwa.

Lallai ba za a yi batun bikin Easter a Ghana, ba tare da bayanin tsaunin Kwahu dake yankin Gabashin kasar ba, inda ‘yan kasa da baki daga kasashen waje suke zuwa, musamman domin shagulgula da suka hada da jerin gwanon kade-kade da raye-raye, da kuma hawa manyan duwatsun Kwahu domin shawagin lema da ake cewa para-gliding a turance.

Easter in Ghana Flying

Sai dai wasu ‘yan Ghana suka ce ba su ji dadin bikin wannan shekarar ba domin yanayin matsin rayuwa. Suka ce, bikin shekarun baya ya fi na wannan shekarar nesa ba kusa ba.

Ga rahoton Idris Abdallah Bako daga birnin Accra:

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Shirin Kammala Bukukuwan Ista A Ghana.MP3