Manyan jam’iyyun siyasa a Nigeria, sun kammala zabukkan su, na tsaida ‘yan takararsu a matakin shugaban kasa, na zaben da za’a yi badi a kasar. A taron da tayi a birnin Fatakwal, babban jam’iyyar adawa ta PDP ta tsaida tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takaranta.
Wanda hakan ke nufi zai kara da shugaba Muhammadu Buhari, idan Allah ya kai rai shekarar 2019, wanda shi kuma jam’iyyar APC ta tabattarda shi a matsayin dan takaranta, an dai tabbatar da shi shugaba Buhari ne a taron da akayi jiya zuwa yau a Abuja.
Daman dai Buhari shi kadai ne dan takaran shugaban kasa a jam'iyyar, da yake bai da abokin takara ko daya. San nan ita kuma jam’iyyar SDP ta tsaida Mr. Donald Duke, a matsayin dan takarar ta a zaben shugaban kasa mai zuwa. A watan Fabrairu mai zuwa ne za a gudanarda wannan zaben.
Your browser doesn’t support HTML5