Ana Shirin Gudanar Da Taron Kolin Jam'iyyar Ma'aikata A Koriya Ta Arewa

Wannan shi ne karon farko da za a gudanar da irin wannan taro cikin shekaru 30, kuma ana sa ran za a gabatar da shugaban kasar na gaba a lokacin

Koriya ta Arewa tana shirin gudanar da gangamin siyasarta mafi girma a cikin shekaru 30, inda ake tsammanin za a ga idanun mutumin da zai zama shugaban kebabbiyar kasar na gaba.

An manna manyan fastoci dake tallata wannan babban taro na jam’iyyar ma’aikata a duk fadin Pyongyang, babban birnin kasar. Kafofin labarai na kasar sun ce wakilan jam’iyyar daga kowane lungu na Koriya ta Arewa su na hallara a Pyongyang domin wannan taro, wanda ake kiran irinsa kawai idan wani batu na gaggawa ko kuma mai matukar muhimmanci ga kasa ya taso.

Masu fashin baki dake sanya idanu kan al’amuran Koriya ta Arewa su na hasashen cewa shugaban kasar mai fama da rashin lafiya, Kim Jong il, zai yi amfani da wannan taron domin damka wani muhimmin mukami na jam’iyya ga dan autarsa, Kim Jong Un, da nufin ya zamo magajinsa a nan gaba.

Babu wani bayanin da duniya ta sani game da Kim Jong Un mai shekaru 27 da haihuwa, sai dai kawai an ce shi ne da na uku, kuma dan lelen mahaifinsa. Kafofin labarai na kasar ba su taba ambaton sunansa ba, kuma babu wani hotonsa da aka sani ko aka gani tun lokacin da ya balaga.

Wannan shine Babban Taro na farko da jam’iyyar ma’aikata zata gudanar tun shekarar 1980, lokacin da aka gabatar da Kim Jong il a zaman mai jiran gadon shugabancin Koriya ta Arewa.

Amma kuma a saboda an saba yin komai cikin sirri a Koriya ta Arewa, ba a fadi ranar da za a fara wannan taron ba, sai dai an ce za a yi shi a farkon watan Satumba kawai.