Ana Shirin Buga Wasan El-Classo Tsakanin Barcelona Da Real Madrid

A yau Laraba 18 ga watan Disamban 2019 za a fafata a babban wasan hamayya na kwallon kafa a kasar Spain bangaren gasar Laliga mai taken El-clasico tsakanin Kulob din Barcelona da Real Madrid.

Wasan da aka yi ittifakin kimanin mutane sama da miliyon 600 zasu kalli wasan a sassa daban daban na duniya, inda aka girke jami'an tsaron fiye da dubu 2800, domin samun tabbataccen kula na tsaro ya yin wasan da zai gudana a Camp Nou.

A baya dai, an sanya ranar 26 ga watan Oktoban bana ne za ayi wasan amman aka dage shi saboda wasu dalilai da ake tunanin za a yi wajen tayar da hankali Kataloniya.

Sai dai a wannan lokaci, dukkanin shugabannin kungiyoyin biyu sun bada tabbacin za ayi wasan lafiya.

Dukkanin yan wasan Barcelona da Real Madrid sun kwana a Otel daya kuma za su tafi filin wasa a tare domin nuna hadin kai a tsakanisu.

A bangaren kocin Real Madrid Zinedine Zidane yace yan wasansa a shirye suke kuma yana da karfin samun nasara a wasan.

Shima a nasa gefen mai horas da kungiyar Barcelona, wacce su zasu karbi bakuncin wasan Ernesto Valverde, ya ce Barcelona ba kanwar lasa bace idan aka duba tarihi.

Wasan za a buga shine da misalin karfe takwas na yammaci agogon Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma kasar Ghana.