Ana Samun Rahotanni Masu Karo Da Juna Kan Tankar Mai Grace 1

Jirgin ruwan Grace 1

Jirgin ruwan Grace 1

Wasu rahotanni masu karo da juna sun kawo rudani jiya Talata kan halin da tankar man nan ke ciki wadda aka kama a kusa da yankin Gibraltar mallakin Burtaniya a watan da ya gabata.

Jalil Eslami, dake zama mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin ruwa ta Iran, ya fadi jiya Talata cewa tankar mai suna Grace 1, nan bada dadewa ba za a sakar wa hukumomin Gibraltar ita.

“Mun yi imanin cewa tankar Grace 1 za ta koma bakin aiki karkashin tutar Iran a ruwan kasa da kasa nan gaba,” a cewar Eslami kamar yadda kamfanin dillancin labaran Iran ya wallafa.

Kamfanin dillancin labaran na Iran, ya ambato wasu hukumomin Gibraltar na cewa za a saki tankar da daren jiya Talata.