Ana Samun Nasara A Yaki Da Kanjamau: NACA

Tambarin yaki da kwayar cutar AIDS

Duk da kalubalen da ake ci gaba da fuskanta na yaduwar annobar Covid-19 a fadin Duniya, gwamnatin tarayyar Najeriya hade da asusun bada tallafi na Majalisar Dinkin Duniya kan cutar HIV/AIDS mai karya garkuwar jikin dan Adam, da dai sauran masu ruwa da tsaki sun yaba tare da jinjinawa hukumar kula da takaita cuta a Najeriya wato NACA bisa jajircewarta wajen ci gaba da bada magani kan cutar a kasar.

Babban Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya, Boss Mustapha, ya sanar yayin gabatar da wata mujalla ta Hukumar mai taken, Kokarin gudanar da aikin magance cutar HIV/AIDS daga shekarar 2007 zuwa shekarar 2021 cewa , hukumar ta NACA ta taka gaggarumin rawa a shekaru 14 da kafuwarta wajen yaki da cutar dake karya garkuwar jikin dan Adam.

corona-ta-sa-an-mance-da-mu---inji-masu-hiv-aids

a-najeriya-masu-cutar-hiv-sun-koka-akan-karancin-magunguna

yaki-da-cutar-aids-na-fuskantar-kalubale-a-najeriya-saboda-janye-wani-tallafi

A cikin watanni 18 da suka gabata, Najeriya ta kara kimanin Mutane dubu 400,000 da aka daura akan maganin kuma mutum dubu 1,000 daga cikinsu sun fito ne daga yankin da aka fi daukar cutar.

Shugaban kwamitin dake lura da ayyukan masu dauke da cutar tarin fuka da cutar ta HIV/AIDS a majalisar wakilan Najeriya Abubakar Sarki Dahiru ya bayyana kudurin gwamnatin kasar na ci gaba da tallafawa wannan bangare. Bisa ga cewar shi gwamnati ta fara ganin nasara a matakan da aka dauka na dakile yaduwar cutar da kuma inganta rayuwar wadanda ke dauke da ita.

A nashi bayanin, darektan asusun bada tallafi na Majalisar Dinkin Duniya kan cutar ta SIDA a Najeriya, Erasmus Morah, ya ce kasar na kan turbar cimma burin da Majalisar Dinkin Duniya ta sa gaba na 90-90-90, wato na tabbatar da cewa kashi 90 na masu dauke da kwayar cutar ta HIV sun san matsayin su, kashi 90 cikin 100 na wadanda ke ɗauke da kwayar cutar suna kan magani yayin da sauran kashi 90 na mutanen dake karɓar magani suna samun sauki.

Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Samun Nasara A Yaki Da Kanjamau-4:00"