"Ana Samun Nasara A Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa A Najeriya"

Hukumomi kan ce hukuncin da wasu manyan 'yan siyasa da jami'an gwamnati da na soji suka dandana saboda laifukan da suka shafi sama da fadi da kudaden al'umma, ya tabbata ne bisa jajircewar gwmanati wajen kawo karshen cin hanci da rashawa. Sai dai wasu kuma na ganin hakan bai wadatar ba.

A wata tattaunawa da ya yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka, Ministan Shari’a kuma Attoni-Janar na Najeriya, Abubakar Malami, ya yi inkarin tambayar da Yusuf Aliyu Harande ya masa akan batun cewa mutane sun dauka tamkar batun yaki da cin hanci da rashawa, ana gafara ne alhalin san ba kaho.

Abubakar Malami, ya kare gwamnati mai ci da cewa lallai tana samun nasara a bangarori da dama da suka shafi batun yaki da cin hanci da rashawa sabanin yadda mutane suke kushe kokarin da gwamnatin ta ke yi.

Ya ce, yarjejeniyar da aka sa wa hannu a wannan ziyarar aiki da suka kai kasar Amurka ta na da nasaba da maido da kudaden da ke da alaka da sama da fadi da dukiyar al’umma. Wannan shaida ne, bisa la’akari da maida kudi dalar Amurka fiye da $300. Malami ya ce, anan, maganar sa ta bayyana ba sauraren gafara ake yi ba.

Ya kuma yi waiwaye izuwa shekara ta 2018, inda ya ce gwamnati ta maido da wasu kudade da ke da nasaba da sama da fadi daga kasar Switzerland, da su ka kai dalar Amurka miliyan dari uku da ishirin da biyu (miliyan $322).

Ya ce, wadannan kudade, su ne kudaden da aka yi amfani da su kan bin da ya danganci EMPOWER (wato kudaden tallafin da ake bai wa wandanda su ka yi karatu suka rasa aikin yi a ko wani wata, su ne kuma kudaden da aka yi amfani da su wajen abun da ya danganci bayar da abinci ga dalibai a makarantu na firamare a duk fadin Najeriya.

Mallam Abubakar Malami, ya zayyana abubuwa da dama da ya ce wadannan abubuwa nasarori ne.

Saboda haka, su talakawa wadanda suka fa’idantu da wadannnan kudade fiye da naira biliyan dari 500, su sun ga san - ba maganar kaho ake yi ba a garesu, inji attoni janar Abubakar Malami.

Ga cikakkiyar hirar da Yusuf Aliyu Harande ya yi da Malami:

Your browser doesn’t support HTML5

Ana samun Nasara Akan Batun Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa