Yanzu haka matsalar ta karancin takardun kudi na CFA ta gurgunta harkokin kasuwanci à wasu jihohin Nijar inda masana tattalin arziki ke gargadi ga hukumomin sojojin Nijar da su samu hanyoyin magance wannan matsalar.
Yan Nijar na nuna damuwa a kan matsalar karancin takardun kudin na CFA da ke zama wata babbar matsala ga harakokin cinakayya a kasar da ta ke neman ta jefa ‘yan Nijar din cikin mawuyacin hali.
An dai dakatar da Nijar daga cikin hada-hadar kudade da kasuwanci a tsakanin kasashen Africa ta yamma rainon kasar Faransa cewa da UEMOA. Tun bayan kifar da gwamnatin Bazoum Mohamed, mafari kenan aka shiga cikin matsalar karancin takardun kudin na CFA wanda har ta kai ga bankuna takaita ma al’umma adadin kudin da zasu iya cirewa daga asusun su na banki, lamarinda ya haifar da fargaba a tsakanin al’umma.
Yanzu haka matsalar karancin takardun kudin na cfa ta soma gurgunta harakokin kasuwanci a wasu sassan kasar ta Nijar, a cewar Muttaha Haruna, wani yan kasuwa a Agadas.
Masana tattalin arziki irinsu Musa Bashir na ganin dole hukumomin mulkin sojin Nijar su samu hanyoyin warware wannan matsalar. Duba da halin da al’ummar kasar zasu shiga sakamakon karancin takardun kudin na CFA.
Nijar ce kasa ta uku da sojoji ke mulki a yammaci Africa baya ga Mali da Burkina Faso. ECOWAS ta sanya takunkuma masu tsauri akan sojojin da su ka yi juyin mulki a Nijar ciki har da hana su anfani da kudaden ajiyarsu na kasashen ketare da ke bakunan shiyyar.
Saurari rahoton Hamid Mahmoud:
Your browser doesn’t support HTML5