Amurka na kiran Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo, da ta bayyana abun da Amurkar ta kira, “Sahihin sakamakon zabe” tare da gargadin cewa za ta ladabtar da duk wanda ya nemi ya yi zagon kasa ga dimokaradiyyar Kongo.
“Wadanda ke kokarin haddasa yamutsi, da barazana ga tsaro ko kwanciyar hankalin Kongo, ko kuma anfana da rashin gaskiya, za a hana masu shiga Amurka; kuma Amurka za ta hana masu duk wani taimakon kudi,” a cewar mai magana da yawun Ma’aikatar Cikin Gida Robert Palladino a jiya Alhamis a wani gargadi.
Shugaban hukumar zabe Corneille Nangaa, ya shaida ma manema labarai a birnin Kinshasa cewa, mai yiwuwa a jinkirta fitar da sakamakon zaben Shugaban kasa na ranar 30 ga watan Disamba, saboda tafiyar hawainiya da aikin kidaya kuri’un ke yi.
Nangaa ya ce an tattara kimanin kashi 20% na kuri’un da aka kada a runfunan zabe a fadin kasar ta yankin tsakiyar Afrika, wadda ba ta da hanyoyi sufuri masu kyau. Ya kuma ce tsarin tattara sakamakon zabe da kuma kidayawa da hannu na kawo cikas da tafiyar hawainiya ga aikin.