Kocin kungiyar kwallon kafa ta Everton Marco Silva, ya bayyana cewar dan wasan tsakiyar kulob din Andre Gomes, zai dawo fagen murza leda a cikin wannan kakar wasan, bayan samu mumunar rauni a wasan da suka tashi 1-1 tsakani su da Tottenham a ranar Lahadi da ta gabata cikin gasar Firimiya lig ta Ingila a bana.
A ranar Litinin data wuce ne akai masa aiki a gwiwar idon sawunsa na kafarsa dama, bayan da dan wasan gaba na Tottenham Son Heung-min ya taho masa ta baya wanda hakan ya janyo masa rauni.
Kungiya tace yanzu komai ya tafi dai-dai tana sa ran dan wasan zai komo wasa nan bada dade wa ba.
Marco ya kara da cewar abune mai wuya su fayyace tabbatar da ranar da dan wasan zai dawo cigaba da wasa, amman bisa irin rahotannin da suka samu daga bangaren masu kula da lafiyar 'yan wasan kulob din, hakan shine zai bamu tabbacin abun.
A wasan da Gomes yaji rauni Alkalin wasan ya bada Jan kati ga dan wasan da suka hadu da Son, inda ya fice daga gasar amma ya nuna damuwarsa sosai a lokacin da ya ga abun da ya faru da abokin wasansu.
Sai dai tuni hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasar Ingila, tayi zama kan Jan katin da aka ba Son, ta kuma janye wannan katin tace tayi haka ne bisa irin yadda dan wasan ya nuna damuwarsa a lokacin da abun ya faru.
Janye Jan katin ya baiwa dan wasan damar ya buga wa Tottenham wasan da tayi tsakani ta da FK Craven Zvezda Belgrade, a gasar zakarun turai, a ranar Laraba kuma ya zura kwallaye biyu wanda bai nuna murna kamar yadda aka saba ganin 'yan wasa keyi in sun ci kwallo su keyi ba.
Wanda hakan yake nuna cewar har yanzu yana nuna alhininsa kan abunda ya faru.