Kungiyar dillalan filayen gini a Jamhuriayr Nijer ta maida martani bayan da gwamnatin kasar ta bayyana shirin rusa gidajen wasu mazauna unguwannin da ke kewayen birnin yamai, wadanda take zargin an gina su ba akan ka’ida ba.
Wakilin Muryar Amurka a Yamai, Sule Mummuni Barama, ya aiko da rahoto cewa wata tawagar Ministocin kasar ce ta gano haramtattun gine-ginen bayan zagaya birnin da ta yi. Ya ce Ministocin sun ce sun gano cewa an yi gine-ginen ne akan filayen da aka ware don amfanar jama’a. Ya ce gwamnati za ta dau matakan da su ka hada da korar wadanda su ka sayi filayen na gwamnati.
Ministan Ayyukan Bunkasa Birane a Nijar, Kassim Mamman Muktar, ya gaya ma Sule Barma cewa an ware irin wadannan filayen ne saboda nan gaba a yi makarantu ko asibitoci ko dandalin wasanni ko gundun kare muhalli da dai sauransu.
To saidai kungiyar masu dillancin filayen ta ce wannan ma bai taso ba, saboda sun bi duk wata ka'ida.
Ga Sule Barma da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5