Ana Neman Diyyar Fiye Da Naira Miliyan 70, A Hannun 'Yan Sanda

Jami'an 'yan sanda sun Najeriya

Majalisar wakilan Najeriya ta umarci kwamitin ta mai bin diddigin korafin Jama’a, ya gudanar da bincike dangane da zargin da ake yiwa ‘yan Sanda a Kano na kisan gilla ga wani mutum mai suna Ibrahim Badamasi na kauyen Gundutse dake yankin karamar hukumar Kura. Al’amarin dai ya faru ne a ranar 14 ga watan Nuwambar bara a yayin arangama tsakanin ‘Yan Shi’a da ‘Yan Sanda akan hanyar Kano zuwa Zaria.

Wasu gungun Lauyoyin kare hakkin bil-Adama ne suka rubuta takardan korafin ga Majalisar wakilan ta Najeriya,suna neman a dauki matakin da yakamata akan ‘yan Sanda, da kuma jami’an kiwon lafiyan da ake zargi da hannu wajan mutuwar wanna magidanci da yam utu yabar ‘ya’ya bakwai da mata biyu.

Garba Ibrahim Diso, dan Majalisar, da ra karata takardan korafin ya ce lauyoyi ne suka rubuto zuwa ga kakakin Majalisar tarayya kuma kakakin ya tura ga kwamitin dake kula da korafe korafe.

Baya ga neman diyyar fiye da Naira miliyan saba’in da biyu, lauyoyin na bukatar a hukunta duk masu ruwa a cikin wannan al’amari.

Da wakilin muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari, ya tuntubi rundunar ‘yan Sandan jihar ta Kano, rundunar tace bata da masaniya akan wanna al’amari.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Neman Diyyar Fiye Da Naira Miliyan 70, A Hannun 'Yan Sanda - 3'18"