Alhaji Aminu Kani daya daga cikin wadanda suke son jam'iyyar PDP ta tsayar dasu takarar gwamnan jihar Jigawa yayi zargin cewa mutum daya tilo ya saye katin duk wakilai da zasu yi zaben fidda gwani ya rabawa nashi yaran.
Sun mika korafinsu ga jam'iyyar inda suka bukaci a bar wakilai su je su zabi dan takarar da suka ga ya cancanta Allah kuma ya baiwa duk mai rabo. To amma idan jam'iyya bata yi masu yadda suke so ba to sai su hakura.
Amma Alhaji Salisu Mamuda shugaban jam'iyyar reshen jihar Jigawa yace sun yi tallar sayar da tikitin wakilan zabe da na 'yan takara. Sun yi sheila a gidan radiyon jihar da ma telebijan. Sun sayarwa wadanda suka je wurinsu saye akan ka'ida kamar yadda tsarin jam'iyyar ya tanada sun kuma sayar masu. An kuma yi sanarwa sau da yawa. Jam'iyyar PDP a jihar Jigawa tayi abun da ya kamata. Ta gudanar da zabuka lafiya kuma ta kammala lafiya lau. Basu da wani dan takara sai wanda walikai suka zaba.
Shi kuwa Onarebu Abba Anas Adamu wanda shi ma yana son ya zama gwamnan jihar a zabe mai zuwa a karkashin laimar PDP yace kowa ya san ba'a yadda mutum ya bayyana ra'ayinsa ba ko ya jawo hankalin mutane akan abun da ba ya kan ka'ida, sai dai kayi shuru. Sule Lamido ya mayar da kansa kamar komi, shi ne wuka shi ne nama.
Onarebul Adamu yace ana bukatar gyara. Misali menen dan adam zai yi ya samu sauki? A ce wai mace mai ciki zata je asibiti ta haihu kyauta ko yaro kasa da shekara biyar zai samu kula a asibiti kyauta ba gaskiya ba ne.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5