Ana Karawa Wurin Fitar Da Zakara A 'Yan Wasan Turai

'Yan wasan Turai

An bayyana jerin sunayen mutum 20 don zaben matashin dan wasan da zai lashe Kyautar Zinare ta 2019, bangaren wasan kwallon kafa ciki har da dan wasan Atletico Madrid mai suna Joao Felix wanda aka nuna a matsayin na gaba gaba cikin sunayen.

An ware kyautar ne musamman ga matasan ‘yan wasa da basu wuce shekaru 21 da haihuwa ba wadanda suke buga wasannin su a nahiyar kasashen Turai. Kuma ‘yan jaridu marubuta labarin wasanni a kasashen nahiyar turai ne suke kada kuri'a yayin zaben.

Dan wasan Felix ya samu kansa cikin jerin sunayen ‘yan wasan ne bisa irin haskakawa da yayi a kungiyarsa ta Benfica, a karkar wasan da ta gabata da kuma wasan da ya buga wa kasar sa Portugal na nahiyar Turai, kafin daga bisani Atletico Madrid ta sayeshi akan kudi yuro miliyon €126.

Matthijs de Ligt shine ya lashe lambar yabo ta karshe a shekarar da ta wuce kuma ya yana cikin jerin ‘yan wasa 20 a wannan shekara.

Ingila tana da wakilai da za'a zaba wada suka hada Jadon Sancho, Mason Mount da kuma Phil Foden, a akwai Matteo Guendouzi na Arsenal sai Moise Kean dan wasan Everton Ga cikekken jerin sunayen yan wasan da kungiyoyin su Matthijs de Ligt ( Juventus) Alphonso Davies ( Bayern Munich) Gianluigi Donnarumma ( AC Milan ) Ansu Fati ( Barcelona) Phil Foden ( Manchester City) Matteo Guendouzi ( Arsenal ) Erling Håland ( Red Bull Salzburg) Kai Havertz ( Bayer Leverkusen ) Joao Felix ( Atletico Madrid ) Dejan Joveljic ( Eintracht Frankfurt ) Moise Kean ( Everton ) Kang-in Lee ( Valencia ) Andriy Lunin ( Real Sociedad ) Danyell Malen ( PSV Eindhoven ) Mason Mount ( Chelsea ) Rodrygo ( Real Madrid ) Jadon Sancho ( Borussia Dortmund ) Vinicius Jr. ( Real Madrid ) Ferran Torres ( Valencia ) Nicolo Zaniolo ( AS Roma