Ana Kara Caccakar Dan Takarar Jam'iyyar Republican Donald Trump

Donald Trump

Caccakar da dan takarar shugaban kasar Amurka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump ya ke sha, ta kara tsanani jiya Talata, saboda sukar wani iyalin Musulmin Amurka wadanda dan su ya mutu yayin da ya ke yaki ma Amurka a Iraki a 2004.

Shugaba Barack Obama ya fada a Fadar Shugaban Amurka ta White House cewa Trump, wanda hamshakin mai hada-hadar gine-gine ne da ya shiga siyasa a karan farko, bai cancanci gadarsa ba a matsayin Shugaban Amurka, kuma in ji Obama, take-takensa na cigaba da jaddada da hakan.

Obama, wanda ya bayyana goyon bayansa ga 'yar takarar jam'iyyar Democrat Hillary Clinton a matsayin wadda za ta gaje shi bayan ya sauka daga mulki, ya kalubalanci 'yan Republican su dawo daga rakiyar Trump, ya ce korafin Trump game da Khizr Khan da matarsa, bayan sun bayyana goyon bayansu ga Clinton a babban taron jam'iyyar Democrat bai dace ba.

Obama ya ce muddun 'yan Republican ba su yi watsi da Trump ba, to korafin da su ke yi game da shi shirme ne kawai.

Da ya ke mai da martani, Trump ya zargi Obama da gazawa a shugabanci. Trump ya ce da Obama da Clinton, wadda ta zama Sakatariyar Harkokin Waje a gwamnatinsa na tsawon wa'adi guda, sun rikida Gabas Ta Tsakiya, su ka sa masu tsattsauran ra'ayi na ISIS su ka mamaye Iraki da Libiya da Siriya.