Hayaniya ta kusa kaurewa tsakanin mambobin kwamiti majalisar dokoki da manyan ma'aikatan hukumar kula da Niger Delta ta NDDC a daidai lokacin da suka gurfana a gaban kwamitin domin kare kasafin kudinsu na shekara 2019.
An shirya sauraren bitar ne kafin a kai ga amincewa da kasafin shekara 2020 inda aka gano cewa Naira biliyan 183 sun yi batan dabo a kasafin bara.
Daya daga cikin 'ya'yan Kwamitin Hon. Shehu Mohammed Wamban Koko, ya ce sun nuna cewa an samu kudaden shiga har biliyan 300 sai suka kashe Naira bilyan 125 amma ba a fadin inda Naira biliyan 183 sukaa shiga ba.
Saboda haka kwamiti ya ce su koma su kawo bitar yadda aka kashe wadanan kudaden amma a ka'ida sai sun sa hannu a takardun da suka kawo saboda a san daga wurin su ya fito.
Sai dai Hon. Babangida Ibrahim mai wakiltar Malunfashi da Kafur ta Jihar Katsina kuma daya cikin 'ya'yan kwamitin ya ce ba a fara bitar kasafin kudi a gama shi rana guda.
Saboda haka, dukkanin abubuwan da wadannan manyan ma'aikata suka kawo ba daidai ba ne, ba su shiryar kasafin daki-daki ba, kuma abu ne da sai an yi bita daya-bayan-daya kafin a kai ga amincewa da shi, saboda haka dole ne a yi gyara in ba haka ba an dinga kai komo kenan.
Su dai shugabannin na hukumar ta Niger Delta sun nemi da a ba su lokaci su koma su sake shiryawa amma 'yan kwamitin majalisar sun dage sai an saka hannu akan bayanan da suka yi kafin su tafi lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce.
A halin yanzu dai an daga zaman Kwamitin har zuwa wani lokaci nan gaba.
Sauraro cikakken rahoton Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5