Ana Kaiwa Filani Harin Sari Ka Noke a Jihar Taraba

Wasu makiyaya

Ana Kaiwa Filani Harin Sari Ka Noke a Jihar Taraba
Harin sari ka noke da Tiv ke kaiwa kan Filani a jihar Taraba ya sa al'ummomin jihar na zaman dar-dar musamman a sassan kudancin jihar.

Maharan suna bin Filanin dake gudun hijira ne daga Benue wadanda gwamnatin jihar Benue ta koro. Hare-haren sun yi sanadiyar asarar rayuka da shanu da suka salwanta. Alhaji Machindo Danburam shugaban kungiyar Miyetti Allah a jihar Taraba ya bukaci a kai masu dauki.

A bayyanin da ya bayar Alhaji Danburam yace maharan daga jihar Benue suke zuwa suna koran shanu kana su kashe masu mutane. A Donga an kashe mutane biyu da Takum inda aka kashe mutane bakwai.

A kungiyance Filanin suna son a yi kiran gaggawa a zauna a tattauna matsalolin domin a yi sulhu. Yace shugabannin Tiv da Filani su zauna su warware matsalarsu cikin lumana domin ya fi kashe juna.

Rundunar 'yansandan jihar Taraba ta tabbatar da harin. Kakakin 'yansandan DSP Joseph Kudi yace yanzu haka an kara tura jami'an tsaro da suka hada da sojoji domin kare rayukan mutane da dukiyoyinsu.

A nashi bayani DSP Kudi yace matsala ce tsakanin Tiv da Filani. Su Tiv din suna shigowa daga jihar Benue su kashe Filani su ma a kashesu. Yace 'yansanda suna aiki dare da rana domin su tabbatar da tsaro da kare doka da oda. Suna sintiri da sojoji da sauran jami'an tsaro.

Kawo yanzu dubban makiyaya ne suka kwararo zuwa cikin jihar kamar yadda sarkin Filanin Wukari Muhammed Musa ya shaida. Yace bayan an koro Filani daga Benue sai kuma Tiv su shigo motoci da bindigogi su kori shanu zuwa jiharsu.

Ga karin rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Kaiwa Filani Hari Sari Ka Noke a Jihar Taraba-3' 16"