Wani babban komandan sojin Amurka dake aiki a Iraqi yace yana hasashen dakarun dake yaki da yan ta’adda a Iraqi zasu sake kwace birane a Mosul da Raqqa daga yan ta’adda cikin watanni shida masu zuwa.
WASHINGTON, DC —
Sojojin Iraqi sune suka sake kwato yankin gabashin Mosul na kogin Tigris kuma ana sa ran zasu kutsa cikin yammacin birnin.
Yace ba wannan ke nufin kungiyar ISIL ta mutuba, har yau suna nan, za su sauya yanayinsu amma ba zasu iya fitowa karara su ce daularsu tana nan tun da yake mun kwace Mosul da Raqqa.
Mosul shine birni mafi girma na biyu a Iraqi kuma birni mafi yawan jama’a da mayakan IS ke rike da shi.
Kakakin rundunar hadin guiwa ya fadawa manema labarai a jiya Laraba cewar suna sa ran wannan yanki da suka kwace daga mayakan IS za a kebe shi a yan makwanni masu zuwa.