Ana tara jerin wadanda za a yi gwajin a kansu da aka ba lakabi REPRIEVE, a wani yunkuri da aka bayyana a matsayin sabon salon yaki da kwayar cutar HIV, da nufin taimakawa wadanda ke dauke da cutar su iya rayuwa cikin koshin lafiya.
Za a kashe dala miliyan ishirin kowacce shekara a kan binciken da Amurka ke daukar nauyinsa, wanda ake kyautata zaton za a dauki shekaru shida ana gudanarwa a kan mutane dubu shida da dari biyar.
Za a rika ba mutanen da za a gudanar da binciken kansu dake kasashen Canada, Thailand, Brazil da kuma Afrika ta Kudu karin kwayar magani guda, banda maganin kwantar da kaifin cutar da suke sha kowacce rana. Maganin zai taimaka wajen rage kwayoyin dake cikin jini dake haifar da hawan jini ko bugun zuciya.
Za a sawa mutanen da ake gudanar da binciken a kansu ido sosai cikin shekaru shida masu zuwa domin ganin ko akwai sauyi a lafiyarsu.