A yayin da aka shiga sabuwar shekara ta 2020, kungiyoyin kwallon kafar nahiyar turai sun dukufa wajen ganin sun inganta kulob-kulob dinsu, domin kammala kakar wasannin bana cikin nasara ta hanyar saye da sayar wa har ma da karban aron 'yan wasa.
A cikin watan Janairun kowace shekara ne, ake bude kasuwar hada-hadar sayen 'yan wasan kwallon kafa ta duniya.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta na yunkurin sayo dan wasan tsakiya na Juventus Emre Can, dan shekaru 25 da haihuwa tare da dan wasan tsakiya na Newcastle United mai suna Sean Longstaff, mai shekaru 22 a duniya.
Arsenal da takwarar karawarta Tottenham sun shiga sahu daya wajen zawarcin dan wasan gefe na kungiyar Atletico Madrid, Thomas Lemar, dan shekaru 24 da haihuwa.
Kungiyar West Ham, ta yunkura don ganin ta dauko dan wasan gaba na Inter Milan dan kasar Brazil, Gabigol mai shekaru 23 da haihuwa.
Inter Milan tana cikin sahun kulob daban-daban da suke sha'awar dauko dan wasan tsakiya na Tottenham, Christian Eriksen, dan shekaru 27.